Gwamnatin tarayya ta sa hannu kan wata yarjejeniyar gina
cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da ruwa da hasken
rana da za ta samar da wuta mai ƙarfin megawatt 20.
Shirin samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 300 wani ɓangare ne na ƙudurin gwamnatin tarayya na komawa ga amfani da makamashi mara gurɓata muhalli.
Za a gina cibiyar a Shiroro da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya kuma zai zama shirin haɗin gwiwa tsakanin kamfanin NSP mai
zaman kansa da hukumar NSIA mai bibiyar harkokin gwamnati Wannan wani shiri ne na farko na samar da lantarki mai amfani da hasken rana da ruwa, kamar yadda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wa Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin da take amfani da makamashi. Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsayayyiyar wutar lantarki tsawon shekaru duk da kasancewarta babbar mai samar da iskar gas da man fetur.














































