Wata motar bas da ke dauke da dalibai daga babbar jami’ar
Kenya ta yi karo da wata babbar mota a kan wani babban titi,
inda 11 daga cikinsu suka mutu, yayin da 42 suka samu
munanan raunuka.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5:50 na yamma a Maungu mai tazara
kilomita 360 daga Nairobi babban birnin kasar. Motar dai na dauke ne da daliban jami’ar Kenyatta da ke kan hanyar zuwa
garin Mombasa da ke gabar teku.
Mahukuntan kasar sun ce ana ruwan sama ne mai karfi, lokacin da direban motar bas din ya yi kokarin wuce wasu jerin motoci. Sai dai motar bas din ta kubce inda ta zarce zuwa gefen dama na titin, Motar bas din tana dauke ne da mutane 58 a lokacin balaguro na ilimi.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta bayyana akan shafinta na X cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti a garin Voi da ke kusa da inda lamarin ya afku














































