Home Labarai Tabarbareawar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyanatukur Mamu A Matsayin Mai Daukar Nauyin Ta’Addanci

Tabarbareawar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyanatukur Mamu A Matsayin Mai Daukar Nauyin Ta’Addanci

139
0

Gwamnatin tarayya ta ayyana sunan Tukur Mamu da karin
wasu mutane 14 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci a
kasar nan.


Wannan bayani na kunshe ne ta cikin wata doguwar takarda da hukumar da ke tattara bayanan sirri kan shige da ficen kudade ta fitar, inda ta ce, cikin mutanen akwai guda 9 da ke da alaka da kasuwanci da kuma 6 da ke hada-hadar sauyin kudade. Hukumar ta ce a wani taro da ta gudanar ta bada jerin sunayen mutanen tare da bada shawarar gudanar da bincike akan su.


Hukumar NFIU ta ce Mamu ya taka rawa wajen samarwa da ‘yan ta’addda kudade ta hanyar karba da kuma kai musu kudaden fansa na adadin kudi dala dubu 200 da ke da alaka da mutanen da kungiyar ISWAP ta sace a jirgin kasan Abuja zuwa
Kaduna.


Cikin sauran mutanen akwai wani mutum da ya kulla tare da samar da kudaden da aka yi amfani da su wajen kai harin ta’addancin da ya faru a Cocin St.Francis Catholic da ke Owo a jihar Ondo da kuma harin da aka kai gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ya faru ranar 5 ga watan Yulin 2022.

Leave a Reply