Home Labaru Majalisar Zartarwar APC Za Ta Nada Sabon Shugaban Bayan Dakatar Da Oshiomhole

Majalisar Zartarwar APC Za Ta Nada Sabon Shugaban Bayan Dakatar Da Oshiomhole

745
0
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Hukunci Kotu: Majalisar Zartarwar APC Za Ta Nada Sabon Shugaban Bayan Dakatar Da Oshiomhole

Majalisar zartarwa ta jam’iyyar APC ta fara tunanin yadda za ta maye gurbin shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole da kotu da dakatar.

Wata majiya ta ce, wasu daga cikin gwamnonin APC sun fara neman wanda mage gurbi Adams Oshiomhole da kotu ta dakatar, aka kuma hana shi shiga ofishin sa da ke Abuja.

Majiyar ta kara da cewa, ana sa ran majalisar zartarwar jam’iyyar za ta kira taron gagagwa, domin samun damar tsaida wanda zai cigaba da shugabantar jam’iyyar a matakin kasa.

Haka kuma, majiyar ta ce akwai yiwuwar jiga-jigan jam’iyyar su nada shugaban jam’iyya na rikon kwarya kafin a kai ga tabbatar da shi a matsayin shugaba mai cikakken iko.

Sai dai, Adams Oshiomhole ta bakin mai magana da yawun sa, Simon Ebegbulem, ya ce ya shigar da kara a kotu domin kalubalantar hukuncin da kotu ta yanke a ranar Larabar da ta gabata.