Home Labaru Safarar Makamai: NDLEA Sun Kama Wata Moto Dauke Albarusai 1,360 A Hanyar...

Safarar Makamai: NDLEA Sun Kama Wata Moto Dauke Albarusai 1,360 A Hanyar Bauchi

470
0
Safarar Makamai: NDLEA Sun Kama Wata Moto Dauke Albarusai 1,360 A Hanyar Bauchi
Safarar Makamai: NDLEA Sun Kama Wata Moto Dauke Albarusai 1,360 A Hanyar Bauchi

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA reshen jihar Bauchi ta yi nasarar kama alburusai dubu 1 da dari 360 a kan hanyar Bauchi zuwa birnin Jos.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar Jonah Achema ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Achema ya kara da cewa, sun samu nasarar kama alburusan ne a cikin wata motar fasinja kirar Vectra, tare da cewa wasu fasinjoji biyu sun amsa cewa albarusan mallakan su ne.

Mutanan sun ce, sun dauko albarusan daga garin Numan da ke jihar Adamawa, kuma za su kai wa wasu da ke siye ne a jihar Filato, sannan sun gaza nuna wata shaida da ta basu damar safarar alburusan.

Kwamnadan hukumar reshen jihar Bauch, Segun Kolawole Oke, ya ce za su mika masu laifin ga rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike a kan su.