Home Labaru Kiwon Lafiya Rashin Cika Al’kawari: Likitoci A Jihar Kaduna Sun Shiga Yajin Aiki

Rashin Cika Al’kawari: Likitoci A Jihar Kaduna Sun Shiga Yajin Aiki

539
0
Rshin Cika Al’kawari: Likitoci A Jihar Kaduna Sun Shiga Yajin Aiki
Rshin Cika Al’kawari: Likitoci A Jihar Kaduna Sun Shiga Yajin Aiki

Kungiyar kananan likitoci ta jihar Kaduna ta fara yajin aikin sai baba ta ji daga ranar Larabar da ta gabata, sakamakon zargin gwamnati da kasa cika alkawari.

shugaban kungiyar Emmanuel Joseph ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a garin Kaduna, inda ya ce sun dauki wannan mataki ne saboda gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na gyara albashin su, tare da magance wasu matsaloli da suka shafi tsarin  kiwon lafiya a jihar.

Joseph ya kara da cewa, sun yanke hukuncin shiga yajin aikin ne, amma duk da haka za su cigaba da kula da marasa lafiya da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, sai dai ba za mu sake karbar wani mara lafiya a asibiti ba, kuma zamu cigaba da sallamar wadanda aka kwantar saboda ba za su iya kula da su ba.

Idan dai ba a manta ba, a watan Oktoban shekara ta 2017 ne gwamnatin jihar Kaduna tare da kungiyar kananan likitocin su ka kulla wata yarjejeniyar warware dukkanin rikicin da ke tsakaninu, tare da sanar da iya lokacin da za a dauka ana aiwatar da al’kawarin domin cimma bukatar yarjejeniyar. A karshe kungiyar ta ce, ta cika alkawarin ta, amma gwmanati ta gaza a nata bangaren, duk da cewa sun tuntubi gwamnatin a ranar 25 ga watan Nuwambar 2019, inda suka ba su wa’adin watanni uku domin su cika alkawarin, amma har yanzu lamarin ya gagara, wanda hakan ya sa suka tsunduma yajin aiki