Majalisar wakilai ta bukaci rundunar soji ta tura karin dakaru
domin samar da tsaro a kan iyakar jihar Sokoto, domin kawo
karshen karbar kudin da ‘yan ta’adan kasashen Jamhuriyar
Nijar da Mali da Libya ke yi a hannun mazauna yankunan da
ke kan iyakokin Nijeriya.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Tangaza da Gudu a jihar Zamfara Sani Yakubu ya gabatar da kudirin, inda ya ce ‘yan ta’addan su na amfani da dazuzzukan Tsauna da Kuyan-Bana wajen aikata ta’addancin su.
Ya ce kungiyoyin ‘yan ta’addan da ke yankin da a baya ba su ga maciji da juna yanzu sun hade wuri guda, inda su ka sha alwashin hana ayyukan noma da kiwo, lamarin da ke kara jefa rayuwar mutanen yankin cikin hadari.
Dan majalisar, ya ce idan har ba a dauki matakan da su ka kamata ba, hakan zai kara haddasa matsalar karancin abinci a sassan Nijeriya, duba da gudunmawar da yankin ke badawa wajen samar da abinci a kasar nan.