Home Labaru Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Tinubu Ya Ciyo Bashin $800m

Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Tinubu Ya Ciyo Bashin $800m

96
0

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar shugaba Tinubu ya
karɓo rancen dala miliyan 800 domin gudanar da shirin samar
da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a Nijeriya.

Haka kuma Majalaisar ta yi gyaran fuska ga dokar ƙarin kasafin kuɗin shekara ta 2022.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya karanto buƙatar shugaban ƙasa a cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar.

Tinubu dai ya ce majalisar zartarwa ta ƙasa a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa Muhammdu Buhari ta amince da karɓo ƙarin rancen dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin aiwatar da shirin tallafin.

Shugaba Tinubu ya ce maƙasudin shirin shi ne domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi su samu abin biyan buƙataun su na yau da kullum.

Leave a Reply