Home Labaru ISWAP Ta Kashe Daya Daga Cikin Ma’aikatan Bada Agajin Da Ta Kama

ISWAP Ta Kashe Daya Daga Cikin Ma’aikatan Bada Agajin Da Ta Kama

314
0

‘Yan kungiyar IS da ke yankin Afirka ta yamma, sun kashe daya daga cikin ma’aikatan jinkai guda shida da aka yi garkuwa da su a watan Yuli.

Dan jarida Ahmad Salkida, wanda ya san yadda kungiyar ke gudanar da al’amuran ta ne ya sanar da haka a shafin sa na Twitter, inda ya ce an harbi ma’aikacin da bindiga a wani faifan bidiyo da ya gani.

Salkida ya kara da cewa, kungiyar ta bada daililin kashe ma’aikacin da cewa, saboda gwamnati ta yaudare su ne sakamakon watannin da aka kwashe ana tattaunawar sirri tsakanin tawagar masu sasantawa da jami;an gwamnati.

Sai dai Salkida bai yi bayani game da yadda ya samu faifan bidiyon ko kuma wurin da aka kashe mutumin ba.

Ahmed Salkida ya kuma wallafa cewa, kungiyar IS da ke yankin Afirka ta Yamma wato ISWAP, ta yi barazanar kashe sauran ma’aikatan agajin a biyar da suka rage a hannun ta.

Leave a Reply