Home Labaru Majalisar Wakilai Ta Ce Sojoji Su Dakatar Da Shirin Tantance Matafiya

Majalisar Wakilai Ta Ce Sojoji Su Dakatar Da Shirin Tantance Matafiya

362
0
Majalisar Wakilai
Majalisar Wakilai

Majalisar wakilai ta bukaci Hukumar Tsaro ta rundunar Sojin Nijeriya ta dakatar da Shirin Tantance Matafiya a kan Tituna da ta yi niyyar farawa a fadin Nijeriya ranar 1 ga watan Nuwamba.

Yayin da Majalisar ta amince da wani uzuri da Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi Elumelu ya gabatar, ta nemi kada sojoji su fara shirin a fadi Nijeriya baki daya.

Elumelu, ya ce shishshigi ne kawai da neman kara dora wa kai wahala, a ce sojoji su kinkimo aikin tare hanyoyi da sunan tambayar katin shaida na matafiya saboda batun tsaro.

Ya ce idan sojoji su ka yi haka, sun tauye hakkin ‘yan Nijeriya da Sashe na 217 na Karamin Sashe na 2 (c da d) a dokar Nijeriya ya ba su.

Shugaban Marasa Rinjayen ya kara da cewa batun katin shaida alhaki ne na Hukumar Bada Katin Shaidar zama Dan Kasa da kuma sauran jami’an tsaro ba sojoji ba.

Dan Majalisa Ahmed Jaha, ya ce wata sabuwar wahala ce da kuma kuntata wa matafiya kawai sojoji ke neman haifarwa a fadi Nijeriya.