Home Labaru Ba A Ce Mu Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi Ba –...

Ba A Ce Mu Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi Ba – Shugaban NYSC

523
0
Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim Shuaibu ibrahim, Shugaban Hukumar Yi Wa Kasa Hidima, NYSC
Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim Shuaibu ibrahim, Shugaban Hukumar Yi Wa Kasa Hidima, NYSC

Shugaban hukumar yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim, ya bayyana halin da ake ciki game da batun karin alawus na Matasan da ke yi wa kasa hidima.

Janar Shu’aibu ya sanar da Manema labarai cewa, kawo yanzu bai samu izni daga Ministar kudi cewa ya soma biyan masu bautar kasa Naira 30,000 kamar yadda aka kara albashi ba.

Shu’aibu Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da Manema labarai, inda ya ce ya tabbatar cewa masu aikin bautar kasa za su amfana da karin albashin.

Ya ce daga cikin hakkokin masu aikin bautar kasa a kan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi akwai wurin kwana da filin noma da tsaro.

Idan dai ba a manta ba, kamar yadda aka tabbatar da karin albashin ma’aikatan gwamnati, Ministan matasa ya bada tabacin cewa za a kara albashin matasa masu yi wa kasa hidima.

Leave a Reply