Home Labaru Kotun Koli Ta Kori Shari’ar Atiku Abubakar Da Shugaba Buhari

Kotun Koli Ta Kori Shari’ar Atiku Abubakar Da Shugaba Buhari

571
0

Kotun koli ta kori karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka shigar su na kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta ba shugaba Buhari na jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2019.

Alkalan kotun dai sun yi watsi da karar ne bisa rashin dacewar ta.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 11 ga watan da ya gabata ne kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da jam’iyyar ta PDP ta shigar ta neman a soke zaben na watan Fabrairu.

Kotun dai ta ce ta yi watsi da karar jam’iyyar PDP ne bisa gaza gamsar da ita a kan korafe-korafen da su ka hada da tafka makudi a zaben shugaban kasa da kuma ikirarin cewa shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takara ba bisa rashin mallakar shedar kammala sakandare ba.

Alkalan kotun, sun ce jam’iyyar PDP ta kasa tabbatar da shaidun da ke nuna ita ce ta lashe zaben na shugaban kasa.

Jam’iyyar PDP da dan takarar ta dai sun daukaka kara a kotun koli ne da nufin kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben shekara ta 2019.

Leave a Reply