Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce alhakin ilmantar da milyoyin yaran da ke yawon almajirci ya rataya ne a wuyan gwamnoni.
Ya ce su ma jihohi su na da masu ilmi da masu fada-a-ji masu ilmin da za su tunatar su kuma fadakar da gwamnonin su dangane da nauyin da ke wuyan su a kan matsalar almajirai.
A cikin wata sanarwa da ya fiytar, mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina, shugaba Buhari ya ce idan akwai tulin almajirai a jiha gwamnati ba ta bin tsarin doka kenan.
Dokar Najieriya dai ta wajabta sama wa yaro ilmi tun daga matakin firamare har har zuwa karamar sakandare kyauta, kuma akasarin yaran da ke barace-barace a kan tituna a Arewacin Nijeirya wadanda ba a dauke su zuwa makaranta ba ne.