Home Labarai Majalisar Harkokin Shari’a Ta Najeriya Ta Nemi A Kori Wasu Alƙalai

Majalisar Harkokin Shari’a Ta Najeriya Ta Nemi A Kori Wasu Alƙalai

209
0
courtss 688508 772421 850x460
courtss 688508 772421 850x460

Majalisar kula da harkokin shari’a a Najeriya ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alƙalai biyu ritaya saboda laifin yin ƙarya a shekarun su na haihuwa.

Cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, majalisar ta (NJC) ta ce ta gano Alƙalin Alƙlai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari’ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifi.

Haka nan majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da na yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.

A cewar sanarwar, binciken NJC ya gano alƙalin alƙalan na Imo na da ranakun haihuwa biyu na 27 ga watan Oktoban 1956 da 27 ga Oktoban 1958.

yayin da shi kuma shugaban kotunan shari’a na Yobe yake da kwanan wata har uku daban-daban.

Bisa wannan dalili ne majalisar ta ce ta ba gwamnatin jihar Imo shawarar yi wa Mai Shari’a Chikeka ritayar dole tare da ƙwace albashin da ya karɓa tun daga ranar 21 ga watan Oktoban 2021.

Leave a Reply