Home Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Karbo Bashin Sama Da Dala Biliyna 2

Gwamnatin Tarayya Za Ta Karbo Bashin Sama Da Dala Biliyna 2

226
0
Wale Edun
Wale Edun

Gwamnatin Tarayya ta amince ta karbo bashi daga kasar waje na dala biliyan 2.2 don bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Ministan Kudi, Wale Edun ne, ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa.

Bayan taron majalisar zartarwa da shugaban kasa, Bola Tinubu ya jagoranta, Edun ya bayyana cewa kudaden za su fito daga Eurobond su ne ($1.7 biliyan) da Sukuk bond ($500 miliyan), sai kuma a jira amincewar Majalisar Dokoki.

Bashin da zai kasance a 2024 kuma wani bangare ne na gyare-gyare domin inganta tattalin arziki da janyo masu zuba hannun jari.

Edun ya kuma bayyana sabon asusun zuba jari na gida na Naira biliyan 250 da aka kafa don samar da lamunin gidaje masu rahusa.

Leave a Reply