Home Home Gwamnatin Jihar Kano ‘Ba Za Ta Yi Katsalandan A Shari’ar Da Ake...

Gwamnatin Jihar Kano ‘Ba Za Ta Yi Katsalandan A Shari’ar Da Ake Yi Wa Murja Kunya Ba’

110
0

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba za ta yi katsalandan a cikin shari’ar da ake yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan Mruja Kunya ba.

Ta kuma ce har yanzu shari’arta ba ta mutu ba, kuma za ta ci gaba har zuwa matakin ƙarshe da kotu za ta yanke hukunci,

Gwamnatin ta ce ta fitar da sanarwar ce saboda An jawo hankalin gwamnatin Jihar Kano kan wani zargi mara tushe da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta kan cewa da hannunta a sakin Murja Ibrahim Kunya da aka yi daga gidan yari, wacce take fuskantar shari’a a kan watsa bidiyon da suka take wasu dokokin jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗannan zarge-zarge kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, wani hasashe ne marar tushe na wasu ɓata-gari da suke so su baƙanta gwamnati da Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf a idon al’umma.

A makon da ya gabata ne Hukumar Hisbah a Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya inda har ta gurfanar da ita a gaban kotu bisa wasu zarge-zarge da suka haɗa da yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.

Leave a Reply