Home Majalisar Dattijan Najeriya Ta Musanta Zargin Almundahana Kan Aikin Hajji

Majalisar Dattijan Najeriya Ta Musanta Zargin Almundahana Kan Aikin Hajji

Kwamitin kula da harkokin wajen Nijeriya na Majalisar Dattawa, ya musanta zargin da wani dan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya yi na almundahana a harkar aikin Hajji.

Shugaban kwamitin Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya musanta zargin, inda ya ce ya tun farko ya shirya sauraren jin ra’ayoyin jama’a a kan hukumar alhazai ta Nijeriya da kyakkyawar niyya, ta neman shawarwarin da za su taimaka wajen inganta ayyukan ta.

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Sokoto ta Kudu Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba dai ya yi zargin cewa, wani bincike da ya gudanar ya gano ana tafka almundahana a harkar aikin Hajji.

Ya ce binciken ya gano ana sama da fadi da kudaden mahajjata, inda masaukin da ya kamata a kama na kwanaki arba’in sai a kama na tsawon kwanaki casa’in, sauran kwanakin kuma sai a sanya Larabawa a dakunan bayan alhazai sun tafi, daga baya a raba kudin tsakanin masu masaukin da shugaban Hukumar Alhazai na wancan lokacin.