Nijeriya ta na shirin gudanar da wani bincike mai zaman kan sa, game da sahihancin rahotannin da ke cewa an samu sinadarin da ke haddasa cutar daji a nau’in taliyar Indomie na ‘Indomie Special Chicken Flavour’.
Rahotanni sun ruwaito cewa, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta tabbatar da shirin gudanar da bincike a kan wannan rahoto.
Lamarin dai, ya biyo bayan matakin da kasashen Malaysia da Taiwan su ka dauka na dakatar da samar da nau’in taliyar a kasashen su, bayan an gano sinadarin da aka ce ya na haddasa cutar daji, wanda ma’aikatun lafiya na kasashen biyu su ka yi a cikin taliyar.
Taliyar Indomie dai ta kasance abincin da ya karade dukkan sassan Nijeriya, inda yara da manya ke tu’ammali da ita a gidajen su a kowace rana.