Home Labaru Zan Biya Ma.aikata Isasshen Albashi – Tinubu

Zan Biya Ma.aikata Isasshen Albashi – Tinubu

1
0

Zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi
alkawarin biyan ma’aikatan Nijeriya albashin da zai ba su
damar yin rayuwa ta mutunci da biyan buƙatun iyalan su.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Twitter domin murnar Ranar ma’aikata ta duniya, Tinubu ya ce zai haɗa hannu da ma’aikata domin a yaƙi talauci da rashin haɗin kai da bambance-banbancen addini a cikin al’umma’ domin tabbatar da ci-gaban Nijeriya baki daya.

Tinubu ya kara da cewa, inganta rayuwar ma’aikata na ɗaya daga cikin muhimman alƙawurran da ya dauka yayin da ya ke yaƙin neman zaɓe, kuma ya bada tabbacin ɗaukar matakai domin ganin ya cika wannan alƙawari.

A karshe Tinubu ya nemi haɗin kan ɗaukacin ‘yan Nijeriya, domin a cewar shi, dole ne a ɗauki tsauraran matakai don a tabbatar ma’aikatan Nijeriya sun samu ƙarin walwala.