Home Labaru Kasuwanci Bunkasa Kasuwanci: Za A Fara Kashe Kudin Najeriya A Kasar China

Bunkasa Kasuwanci: Za A Fara Kashe Kudin Najeriya A Kasar China

18
0

Bankunan kasar China za su fara karbar kudaden Najeriya nan gaba, kuma bankunan China za su shigo Najeriya domin fara aiki.

Jakandan kasar China a Najeriya, Cui Jianchun, ya sanar da hakan I inda yace hakan zai taimaka wajen bunkasawa tare da saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce ofishinsa na aiki tukuru domin tabbatar da ganin bankunan Najeriya sun fara aiki a kasashen biyu, inda “Manyan bankunan kasashen biyu ke kokarin fara aiwatar da yarjejeniyar amfani da kudaden.

Ya kara da cewa “Yanzu haka yana aiki domin ganin bankunan kasar sun shigo Najeriya sun fara aiki, yayinda a daya bangaren bankunan Najeriya ma suke gaba da aiki a China.

Azantawarsa da manema labarai a nan Abuja, yace hakan zai saukaka amfani da kudaden China da Najeriya inda ya yi fatan samun fahimtar juna tsakananin majalisun dokokin kasashen biyu a kan lamarin.