Majalisar Dattawa ta amince da kasafin naira tiriliyan 21 da biliyan 800, wanda ke nuni da cewa sun yi ƙarin har naira tiriliyan 1 da biliyan 300 a kan naira tiriliyan 20 da rabi da Shugaba Muhammadu Buhari ya kasafta a cikin watan Oktoba.
Yanzu haka dai kasafin zai koma naira naira tiriliyan 21 da biliyan 827 da miliyan 188 da dubu 747 da 391.
‘Yan majalisar, sun ƙara gejin farashin fetur a ma’aunin kasafin kuɗi, da kuma ma’aunin kasafin kuɗi bisa mizanin farashin gangar ɗanyen mai a duniya.
An dai tsara kasafin Nijeriya a kan mizanin yawan gangar ɗanyen man da ake haƙowa a kowace rana, wato ganga miliyan 1 da dubu 600.
‘Yan Majalisar, sun amince da kasafin ne bayan da Shugaban Kwamitin Kasafi na majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin ya damƙa wa majalisa rahoton sa, wanda ya kunshi ƙarin naira Miliyan 967 a ɓangaren da kasafin majalisar dattawa ke ciki.