Home Home Gobara Ta Lalata Gidaje, Mutane Sun Bace A Ribas

Gobara Ta Lalata Gidaje, Mutane Sun Bace A Ribas

110
0

Sama da mutane 200 ne sun bace, yayin da kadarori na miliyoyin naira su ka kone kurmus sakamakon tashin gobara a yankin Elekahia na Jihar Rivers.

Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Juma’ar nan, wanda ake zargin kalanzir ne ya haddasa tashin gobarar.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun tafi hutun bikin karshen shekara, yayin da wasu kuma ke wuraren aiki lokacin da lamarin ya auku. Jami’in hukumar kashe gobara ta jihar John Nnemeka, ya ce sun isa wurin da lamarin ya faru, amma sun gaza shiga sakamakon yanayin yadda gine-ginen gidajen su ke.

Leave a Reply