Home Home Ku Nemi Makamai Don Kare Kanku Daga Hare-Haren ‘Yan Bindiga – Gwamnan...

Ku Nemi Makamai Don Kare Kanku Daga Hare-Haren ‘Yan Bindiga – Gwamnan Bauchi

150
0
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya umarci al’umomin yankunan da aka kai wa hari a yankin ƙaramar hukumar Alkaleri su nemi makamai domin su kare kan su daga harin ‘yan bindiga.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya umarci al’umomin yankunan da aka kai wa hari a yankin ƙaramar hukumar Alkaleri su nemi makamai domin su kare kan su daga harin ‘yan bindiga.

Bala Muhammad ya bayyana haka ne a fadar hakimin Yelwan Duguri, lokacin da ya ziyarci ƙauyukan Rimi da Gwana da Yelwan Duguri domin jajenta masu a kan hare-haren ‘yan bindiga.

Dagacin garin Yelwan Duguri Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya ce mutane 20 ne su ka mutu a ƙauyen Rimi lokacin da ‘yan bindigar su ka kai hari.

Gwama Bala, ya ce lamarin abu ne da ba za a lamunta ba, don haka dole a yi duk abin da ya kamata domin hana faruwar haka a nan gaba.

Leave a Reply