Majalisar ta yafe wa Sanata Ningi tare da janye dakatarwar da ta yi masa
an ɗauki matakin ne bayan Sanata Moro ya gabatar da ƙudirin neman afuwar a madadin sa kuma ya ɗauki alhakin dukkan abin da ya faru a zaman da suka.
Shugaban Majalisar Akpabio ya siffanta sanata Abdul Ningi a matsayin mutum mai hazaƙa kuma ya ce sun ɗauki matakin ne ba tare da nuna ɓangaranci ba.
Dakatarwar da aka yi wa sanatan mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya ta tsawon wata ta jawo cecekuce a majalisar da ma
faɗin ƙasa a watan Maris.
Ƙudirin da majalisar ta zartar a lokacin ya zargi Abdul Ningi da zubar da ƙimar majalisa
bayan ya zargi shugabannin ta da sake yin wani kasafin kuɗi na 2024 bayan wanda ‘yan majalisar suka amince da shi a bainar jama’a.














































