Home Labarai PDP Za Ta Tantance Masu Neman Tikiti 17 A Ranar Juma’a Mai Zuwa

PDP Za Ta Tantance Masu Neman Tikiti 17 A Ranar Juma’a Mai Zuwa

29
0

A ranar Juma’a mai zuwa ne, jam’iyyar PDP za ta tantance ‘yan takara 17 da ke fafutukar mallakar tikitin takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023.

Tsohon shugaban majalisar dattawa Cif David Mark, shi ne
shugaban kwamitin mutane tara da za su gabatar da shirin
tantance ‘yan takarar.

Daga cikin ‘yan takarar da za a tantance kuwa akwai Tsohon
mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da Tsohon
shugaban majalisar dattawa sanata Bukola Saraki, da Tsohon
gwamnan jihar Anambra Peter Obi da Gwamnan jihar Sokoto
Aminu Waziri Tambuwal.

Sauran sun hada da Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Pius
Anyim, da Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike.

Jadawalin ayyukan da sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar
Bature ya fitar ya nuna cewa, za a gudanar da taron tantancewar
ne a helkwatar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar
da ke Legacy House a Abuja.