Home Labaru Majalisa Za Ta Kashe Naira Biliyan 37 Wajen Gyaran Zaurukan Ta

Majalisa Za Ta Kashe Naira Biliyan 37 Wajen Gyaran Zaurukan Ta

479
0

Majalisar dokoki ta tarayya, ta amince da kashe naira biliyan 37 domin gyaran zaurukan majalisar, yayin da ta kebe naira biliyan daya domin gudanar gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Nijeriya da ake sa ran farawa a farkon shekara mai kamawa.

Daraktan yada labarai na majalisar dokokin Dr. Rawlings Agada ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 8 ga watan Oktoba na shekara ta 2019 ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin shekara ta 2020 ga majalisar dokoki ta tarayya.

Sai dai kuma ‘yan majalisar sun kara kusan naira biliyan 30 a kan kasafin da shugaba Buhari ya gabatar.

Leave a Reply