Home Labaru Majalisa Ta Zargi Malami Da Yi Mata Katsalandan

Majalisa Ta Zargi Malami Da Yi Mata Katsalandan

80
0

Kwamitin Majalisar Wakilai ya zargi Babban Lauyan Tarayya Abubakar Malami, da jami’an hukumar ‘yan sandan kasa da kasa Interpol a kan yi masa katsalandan a binciken da ya ke gudanarwa.

Haka kuma, Kwamitin mai bincike a kan badaƙalar satar ɗanyen mai tun daga shekara ta 2014, ya ce bai ga dalilin da zai sa jami’an Interpol a bisa buƙatar Ma’aikatar Shari’a su ka yi ma wanda ya yi fallasa tambayoyi bayan Majalisar ta fara gudanar da binciken ta ba.

Kwamitin dai ya na bincike a kan zargin da aka kwarmata na saida wa Chana ɗanyen mai ganga miliyan 48 mallakar Nijeriya ta haramtacciyar hanya a shekara ta 2015, wanda kuɗin ya kai Dala biliyan 2 da miliyan 400.

Sai dai shugaban hukumar Interpol ta ƙasa Garba Umar, ya ce hukumar ta yi aiki ne bisa buƙatar Babban Lauyan tarayya.

Shugaban Kwamitin Bincike a kan satar mai Mark Gbillah, ya ce, akwai wata ƙungiya mai suna Advocacy for Good Governance and Free Nigeria, wadda ta aike wa Babban Lauyan wasiƙa, ta na mai sanar da shi cewa akwai wani gungun masu ɓata suna da ke ƙoƙarin ɓata sunan manyan jami’an gwamnati.