Home Labaru Atiku Ba Zai Ci Zabe Ba — Edwin Clark

Atiku Ba Zai Ci Zabe Ba — Edwin Clark

31
0

Dattijo Edwin Clark, ya bukaci Gwamnan jihar Delta ya yi hasashen cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da abokin takarar sa Ifeanyi Okowa ba za su ci zaben da ke tafe ba.

Edwin Clark, ya kuma bukaci Gwamnan Ifeanyi Okowa, ya janye takarar sa ta mataimakin Atiku Abubakar.

Mista Clark, ya zargi Okowa da amfani da dukiyar yankin Neja Delta wajen yakin neman zaben Atiku, inda ya bukaci gwamnan ya fito ya ba al’ummar Kudu hakuri ya kuma janye takarar sa.

Dottijon ya bayyana haka ne, a cikin wata wasika da kungiyar PANDEFF ta aike wa Okowa, wadda aka karanto a wajen wani taron manema labarai a Abuja.

A cewarsa, Okowa ya saba wa matsayar da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin, na kin mara wa duk wani dan siyasa da bai fito daga yankin su baya ba, musamman ma Atiku Abubakar.