Home Labaru Majalisa Ta Tara: A Yau Talata Majalisar Zata Fara Aiki Da Zarar...

Majalisa Ta Tara: A Yau Talata Majalisar Zata Fara Aiki Da Zarar An Kammla Zabe

308
0

Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Tara Zata Fara Aiki Da Zarar An Kammala Zaben Shugabannin Majalisara Yau Talata 12 Ga Watan Yunin Shekara Ta 2019.

Kawo Yanzu Daishirye-Shirye Sun Kammala Don Kaddamar Da Majalisun Dokokin Nijeriya A Karo Na Tara, Jam’iyyar APC Da Ke Da Rinyaye Ta Kara Jajircewa Domin Ganin ‘Yan Takarar Da Ta Tsaida Sanata Ahmed Lawan A Majalisar Dattawa Da Femi Gbajabiamiala A Majalisar Wakilai Su Samu Nasara.

Tsohuwar Majalisa Ta Takwas Ta Kammala Aiki A Makon Jiya Ne, Inda Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki Ya Ba Kowa Dama Ya Yi Takarar Yadda Ya Ke Ganin Majalisar Ta Gudanar Da Aiki A Tsawon Shekaru Hudu.

Tsohon Shugaban Kwamitin Yada Labarai Namajalisar Wakilai Ta Takwas, Abdulrazak Namdas, Na Daga Cikin Wadanda Su Ka Janye Daga Takarar Kakakin Majalisar, Domin Marawa Muradun Jam’iyyar Sa Ta APC Baya.