Home Labaru 12 Ga Watan Yuni: Gwamnatin Tarayya Ta Ceta Zama Ranar Hutun Dimukradiyya

12 Ga Watan Yuni: Gwamnatin Tarayya Ta Ceta Zama Ranar Hutun Dimukradiyya

272
0

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Laraba 12 Ga Watan Yuni A Matsayin Ranar Hutun Murnar Ranar Dimokuradiyya A Nijeriya.

Hakan Ya Biyo Bayan Dokar Da Gwamnatin Ta Kafa Ne Na Maida Ranar 12 Ga Watan Yunin Kowace Shekara A Matsayin Ranar Dimokuradiyya.

Babbar Sakatariya A Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje Georgina Ekeoma Ehuriah Ta Bayyana Haka A Madadin Gwamnatin Tarayya A Cikin Wata Sanarwar Da Daraktan Yada Labarai Na Ma’aikatar Mohammed Manga Ya Sanyawa Hannu.

Ehuriah Ta Kuma Taya Dukkanin ‘Yan Nijeriya Da Ke Gida Da Kuma Kasashen Wajemurna A Kan Tabbatuwan Mulkin Dimokuradiyya A Nijeriya.

Sannan Ta Yi Kira Ga ‘Yan Nijeriya Su Ci Gaba Da Yin Madalla Da Sadaukarwar Da Zaratan Nijeriya Su Ka Yi Na Gwagwarmayar Tabbatuwar Mulkin Dimokuradiyya Wanda Hakan Ya Sa Suka Rasa Rayukan Su Domin Ganin Nijeriya Ta Tsaya Da Kafafun Ta.

Barista Ehuriah, Ta Kuma Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Hada Kai Tare Da Ba Gwamnatin Buhari Goyon Baya Domin Ganin Ta Cimma Nasarorin Da Ta Sa A Gaba, Musamman Na Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa Da Samar Da Zaman Lafiya Da Dai Suran Su.