Majalisar Dokokin Tarayya ta mika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kasafin kudin kasar na badi domin ya rattaba hannu a kai.
Wata majiya daga ofishin Magatakardan Majalisar da ta tabbatar da hakan, ta ce an mika wa shugaban kasar kasafin kudin ne tun a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamban 2021.
A cewar majiyar, ana sa ran Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin kafin ranar 31 ga watan Disamban 2021, a yayin da za a yi bankwana na karshe da shekarar.
Tun a ranar Lahadi, 26 ga wata aka mika wa shugaban kasa kasafin kudin.
Majiyar ta kuma karyata rade-radin da suka rika yaduwa a bayan nan cewa ba a aike wa shugaban kasa kasafin kudin ba yayin da ya rage kwanaki uku a yi bankwana da shekarar 2021.
Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne zauren Majalisun Tarayya biyu da suka hada da na Wakilai da Dattawa suka amince da kasafin kudin na badi gabanin su tafi hutun su na karshen shekara.














































