Home Labaru Ministan Shari’A Ya Ce Sabuwar Dokar Zabe Rudu Kawai Za Ta Haddasa

Ministan Shari’A Ya Ce Sabuwar Dokar Zabe Rudu Kawai Za Ta Haddasa

94
0

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce sabuwar dokar zabe da ake ci gaba da cece-kuce kanta, za ta iya haddasa ruduni ne kawai da kashe makudan kudade, don haka ya sa shugaba Buhari ba zai sanya mata hannu ba.

A yayin wata zantawa da wani gidan rediyo a Kano, Ministan ya ce dokar za ta kuma kara ta’azzara kalubalen rashin tsaro, haka kuma ba ta wakilcin ra’ayin akasarin ‘yan Najeriya.

Idan za’a iya tunawa shugaba Buhari ya ki amincewa da sanya hannu kan dokar bayan da majalisar dokoki zartar da ita, inda ya rubuta wasika ga majalisar yana baiyana dalilan jingine dokar.

An sami ‘yar muhawara a tsakanin ‘yan majalisar inda su ka ce za su tuntubi jama’a a hutun da su ka shiga yanzu in sun dawo su dauki matsayar amincewa da dokar ko akasin hakan.

Leave a Reply