Home Labarai Fadowar Kankara: Jihohin Yammacin Amurka Na Cikin Duhun Rashin Lantarki

Fadowar Kankara: Jihohin Yammacin Amurka Na Cikin Duhun Rashin Lantarki

80
0

Kanƙara ta lulluɓe yankin yammacin Amurka, inda ta jefa
dubbai cikin duhun rashin lantarki.

Kankara mai tudun inci 30 ne ta yi ta faɗowa a arewacin
California cikin awa 24, hakan ya jawo ɗaukewar lantarki da
kuma rufe Tituna.

A ranakun karshen mako ma, guguwa haɗe da ambaliyar ruwa ta
afka wa kudancin Carlifornia, wadda ta lalata lantarki da kuma
cika tituna da ruwa.

Hukumar yanayi ta ƙasa ta ce ruwan sama mai tudun inci 1.8 zai
ci gaba da zubowa a Reno, da Navada daga Lahadi da dare zuwa
Litinin din nan.