Home Labaru Majalisa Ta Fara Shirin Halasta Wa Matuƙa Mota Amfani Da ‘Bluetooth’

Majalisa Ta Fara Shirin Halasta Wa Matuƙa Mota Amfani Da ‘Bluetooth’

114
0

An gabatar da sabon ƙudirin halasta wa matuƙa mota yin amfani da na’urar sarrafa kira da amsa kira da sauraren kaɗe-kaɗe wato ‘Bluetooth’ idan su na tuƙi.

Sai dai ƙudirin idan ya samu karɓuwa, zai kasance sai matuƙin motar da ya haura shekaru 21 ne zai samu damar amfani da wannan doka.

Ɗan Majalisa Ibrahim Hamza na jam’iyyar APC daga jihar Kaduna ya gabatar da ƙudirin, wanda ya amince da sai direbobin da su ka haura shekaru 21 a duniya ne dokar za ta amfana.

Kudirin dai, zai yi ƙoƙarin maye gurbin Sashe na 10 (4) na Dokar Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa, yayin da  shigo da dokar zai sa direba ya riƙa waya a lokacin da ya ke tuƙi, amma ta hanyar yin amfani da na’urorin da ba sai ya ɗaga waya ba.

A cikin sabon ƙudirin, waɗanda ba a amince su yi amfani da waya ba a lokacin da su ke tuƙi, sun haɗa da direbobin motocin ɗalibai da na manyan motoci.