Home Labaru Kotu Ta Dage Sauraren Karar Kisan Hanifa A Kano

Kotu Ta Dage Sauraren Karar Kisan Hanifa A Kano

48
0

Kotun majistare da ke sauraren karar kisan da aka yi wa Hanifa Abubakar Kano, ta bada umarnin ci-gaba da tsare wadanda ake zargi da kisan har zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu na shekara ta 2022.

Lauyoyin gwamnati a karkashin jagorancin Barista A’isha Mahmud ne su ka nemi a sake tsare mutanen, har zuwa lokacin da za su gurfanar da su a wata babbar kotu da ke da hurumin sauararen karar.

An dai kai babban wanda ake zargi da kisan, kuma mai makarantar marigayiyar Abdulmalik Tanko tare da sauran mutane uku gaban kotun majistaren a Gidan Murtala da ke birnin na Kano.

A farko-farkon watan Janairu ne aka gano gawar Hanifa, bayan sace ta da kuma hallaka ta ta hanyar ba ta maganin kashe bera a cikin shayi.