Home Labaru Majalisa Ta 9: Ndume Ya Yi Watsi Da Bukatar APC Na Tsaida...

Majalisa Ta 9: Ndume Ya Yi Watsi Da Bukatar APC Na Tsaida Ahmad Lawal Shi Kadai Tilo

290
0

Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a
zauran majalisar dattawa Ali Ndume ya ce zai yi watsi da
maganar shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole
ya nemi takarar shugaban majalisar.
Bayan sanata Ali Ndume na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake
shirin gudanar da zaben shugabannin majalisar tarayya ta 9,
wanda hakan ke nuna cewa akwai rikici mai karfi da zai iya
kunnu kai a cikin gidan jam’iyyar APC.
Ali Ndume ya nuna cewa, sam bai damu da bayyana Ahmad
Lawan da jam’iyyar APC ta yi a matsayin wanda zai gaji Bukola
Saraki ba, sai dai shima yana nasa shirin na neman kujerar.

Sanata Ali Ndume ya gabatar da wasu manufofi 9 da ya ce idan
ya samu kujerar shugaban majaliar dattawa zai dabbaka su
domin samun cigaban a Nijeriya, tare da yin aiki da shugaban
kasa sau-da-kafa.
Idan dai ba a manta ba, matsayar jam’iyyar APC shi ne babu
wanda zai yi takara da Ahmad Lawan, wanda kuma shi Ali
Ndume ke ganin hakan ba dai-dai ba ne, domin ya sabawa tsarin
majalisa da dokar kasa wanda hakan ya sa ya ke fito-na-fito da
jam’iyyar.