Home Labaru Majalisa Ta Ƙalubalanci Amaechi A Kan Gina Titin Jirgin Ƙasa Na Kano...

Majalisa Ta Ƙalubalanci Amaechi A Kan Gina Titin Jirgin Ƙasa Na Kano Zuwa Maraɗi

80
0

Kwamitocin sufurin kasa da na ruwa na Majalisun dokoki na tarayya, sun soki shirin ministan sufuri Rotimi Amaechi na gina sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Kano zuwa Maraɗi, yayin da za a gina ƙaramin titin a sauran sassan Nijeriya.

‘Yan majalisar dai sun fusata, lokacin da Amaechi ya miƙa kasafin kuɗin ma’aikatar sa na shekara ta 2022 a gaban kwamitocin.

Rotimi Amaechi, ya ce titin mai nisan kilomita 284, zai haɗa Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika ta Yamma.

Shugaban kwamitin sufuri na majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje, da na majalisar wakilai Mista Pat Asadu, sun yi fatali da abin da su ka kira nuna wariya ga sauran yankunan Nijeriya a batun gina titin jirgin.

Shugabannin kwamitocin biyu, sun buƙaci ministan ya bayyana dalilin da ya sa ba za a gina tituna iri daya a faɗin ƙasar nan ba.

Pat Asadu, ya nemi Amaechi ya bayyana dalilin da ya sa zai gina titin jirgin ƙasa na zamani mai nisan kilomita 284 da kuɗin Nijeriya, wadanda aka aro saboda ‘yan Nijeriya zuwa Jamhuriyar Nijar, yayin da za a yi gyara tare da sake gina ƙaramin titin jirgin ƙasa daga Maiduguri zuwa Fatakwal.