Home Labaru Taron Majalisar Zartaswa Ya Amince A Kashe Naira Biliyan 47 Kan Wasu...

Taron Majalisar Zartaswa Ya Amince A Kashe Naira Biliyan 47 Kan Wasu Ayyuka

52
0

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ta amince a kashe Naira biliyan 47 domin gudanar da kwangiloli a ma’aikatun sufurin jiragen sama da na ayyuka da gidaje da kuma hukumar kwastam ta Nijeriya.

Bayanin hakan ya fito ne, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar, wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya jagoranta a Abuja.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ya ce an amince da takardun da ya gabatar, wadanda su ka hada da na sayen kayan aiki na kimanin Naira Biliyan 28 da Miliyan 39 da dubu 80 da 799 da Kobo 40 wajen kawo na’urorin zamani.

Sauran kwangilolin sun hada da na’urorin da za a sa a filayen jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas, da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, wadanda za su lakume Naira biliyan 5 da Miliyan 800.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce majalisar ta amince da kwangilar gina sabon ginin majalisar dattawa da kayayyakin da za zuba a ciki, da kuma gina dakin taron da zai dauki mutane dubu daya a jami’ar Abuja, kwangilar da ya ce za a bada a Naira Biliyan 2 da Miliyan 354 da dubu 247 da 466 da Kobo 76.