Home Labaru Ginin Da Ya Rushe A Legas Ba Nawa Ba Ne – Osinbajo

Ginin Da Ya Rushe A Legas Ba Nawa Ba Ne – Osinbajo

11
0

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya musanta zargin cewa ginin da ya rushe a Legas mallakin sa ne.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Laolu Akande ya fitar, ta ce masu son tada zaune tsaye ne ke yaɗa wannan jita-jita.

Sanarwar ta kara da cewa, Osinbajo ba ya da alaƙa da filin ko kuma ginin, kamar yadda wasu ke cewa ya sayi filin ne daga hannun Shugaban kamfanin motoci na Elizade Motors Cif Michael Ade.

Ya ce masu yaɗa jita-jitar ba su yi la’akari da halin baƙin cikin da mutanen da su ka rasa ‘yan’uwa a rushewar ginin ke ciki ba.

Farfesa Osinbajo dai ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda su ka rasa rayukan su da waɗanda su ka jikkata a lamarin.