Home Home Majalisa Na Zargin Minista Malami Da Karkatar Da Dala Miliyan 200, Kuma...

Majalisa Na Zargin Minista Malami Da Karkatar Da Dala Miliyan 200, Kuma Ya Ƙi Amsa Gayyata

467
0

Kwamitin Binciken Salwantar Maƙudan Kuɗaɗe na majalisar wakilai, ya gayyaci Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Kuɗi Zainab Ahmed su bayyana a gaban shi domin su yi bayani a kan yadda aka yi Ofishin Ministan  ya amince a biya wasu ‘yan kwangilar da ba a san su ba har dala miliyan 200.

Tuni dai Kwamitin ya yi barazanar cewa ba sau ɗaya ba ya gayyaci ministocin biyu ba amma sun ƙi bayyana, don haka zai umarci a kamo ‘yan kwangilar da aka ce an ba kuɗaɗen da kuma ministocin biyu.

Da farko dai wani ne ya tsegunta wa Hukumar Sa-ido a Kan Hada-hadar Kuɗaɗen Gwamnati, cewa an biya wasu kamfanonin bogi har dala miliyan 200 a matsayin sun yi aikin tuntuɓa bisa amincewar Ofishin Ministan Shari’a da Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai tsegumin ya ce an biya kuɗaɗen a kamfanoni biyu, kamar yadda Shugaban Kwamitin Majalisar Mark Gbillah daga Jihar Benue ya bayyana.

Shugaban Kwamiti ya ce su na zargin sace kuɗaɗen aka yi, domin ta Ofishin Ministan Shari’a aka karkatar da sun, alhalin ba ya da ikon kashe wa Nijeriya kuɗaɗe ko ikon bada umarnin a kashe kuɗin Nijeriya, domin doka ba ta ba shi wannan ƙarfin ikon ba.

LEAVE A REPLY