Home Home El-Rufai Ya Nada Sabbin Alkalai 15 Kasa Da Kwana 35 Ya Mika...

El-Rufai Ya Nada Sabbin Alkalai 15 Kasa Da Kwana 35 Ya Mika Mulki

307
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya rantsar da sabbin alkalai 15 da ya nada a kotunan jihar daban-daban.

Wadanda aka rantsar sun hada da alkalan babbar kotun jihar Kaduna guda bakwai, da na kotun daukaka kara na shari’a guda biyar, da kuma alkalan kotun daukaka kara guda uku.

Alkalan babbar kotun sun hada da Bashir Shitu Yusuf, da Yakubu Badamasi da Abdullahi Isyaka da Joyce Asabe Aka’ahs da Nana Fatima Muhammad da Ambi John Aku da Buhari Mohammed Balarabe.

Wadanda aka rantsar a matsayin alkalan kotun daukaka kara ta Shari’a kuma sun hada da Aminu Ahmad Jumare da Nuhu Mahmud da Murtala Nasir da Abdulrahman Ibrahim da Suraj Mahadi Mohammad. Alkalan kotun daukaka kara kuma sun hada da Dorothy Sim Inwulale, da Dorcas Thabita Antung da kuma Yusuf Yakubu.

Leave a Reply