Home Home Mamakon Ruwan Sama Ya Tafi Da Gidaje Da Dama A Jalingo

Mamakon Ruwan Sama Ya Tafi Da Gidaje Da Dama A Jalingo

55
0

Ruwan sama mai karfi ya shanye gidaje da dama a birnin Jalingo na jihar Taraba.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da kogin Mayo Gwoi ya tunbatsa, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka ɗauki tsawon sa’o’i biyu ana tafkawa.

Rahotanni sun ruwaito cewa, gidajen da ambaliyar ta shafa su na kusa da gabar kogin ne.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma ambaliyar ta lalata dukiyoyin da su ka haɗa da kayan gida da kayayyakin abinci na miliyoyin naira.

Leave a Reply