Home Labaru Karin Albashin : Gwamnoni 9 Na Tare Da Kudurin Shugaban Kasa

Karin Albashin : Gwamnoni 9 Na Tare Da Kudurin Shugaban Kasa

301
0

Wasu gwamnoni 9 sun ce a shirye suke domin fara biyan mafi karancin albashi na naira duba 30 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu.
Gwamnonin sun hada da na jahohin Kano, Zamfara, Kwara, Delta , Rivers, Kogi da Neja da Osun da Rivers da kuma Edo, inda suka kara da cewar kyautatawa ma’aikata shin babban burinsu.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari sun ce babban burin gwamnatin su, shi ne ta ga ma’aikatan jihar na walwala.
Haka zalika ita ma gwamnatin jihar Osun da ta jihar Kogi sun ce za su jira su ga tsare-tsaren da za abi domin fara biyan ma’aikatan naira dubu 30.
Gwamnatin jihar Kogi da ta Neja sun ce tun da gwamnatin tarayya ta mayar da karin albashin doka a shirye suke su biya albashin.
Ita ma gwamnatin jihar Delta da Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da kuma na jihar Edo dukkannin sun ce suna jira gwamnatin tarayya ne kawai ta fitar da tsare-tsare yadda za a biya ma’aikatan domin fara aiki dashi.

Leave a Reply