Home Labaru Harin Afghanistan: Kwamitin Sulhu Ya Bukaci Hukunta Wadanda Aka Kama

Harin Afghanistan: Kwamitin Sulhu Ya Bukaci Hukunta Wadanda Aka Kama

64
0
Afghanistan

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen duniya da suyi aiki tare wajen ganin an zakulo wadanda suka kai harin ta’addanci birnin Kabul dake Afghanistan domin hukunta su.

Sanarwar da wakilan kwamitin 15 suka rattabawa hannu ta jaddada muhimmancin hukunta wadanda suka shirya da kuma kai harin tare da wadanda suka dauki nauyin sa.

Kwamitin ya bukaci daukacin kasashen duniya da suyi aiki tare da dokokin da aka tanada tare da kudirorin Kwamitin sulhun domin samun nasara akai.

Akalla mutane kusan 100 suka mutu sakamakon kazamin harin cikin su harda sojojin Amurka 12, abinda ya sa shugaba Joe Biden ya alwashin farautar wadanda ke da hannu a harin domin hukunta su.