Home Labaru Maharan Da Su Ka Sace Dalibai A Nasarawa Sun Nemi Naira Miliyan...

Maharan Da Su Ka Sace Dalibai A Nasarawa Sun Nemi Naira Miliyan 25

12
0

Rahotanni daga jihar Nasarawa na cewa, maharan da su ka sace mutane 4 a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Mararrabar Akunza, sun tuntubi iyalan su tare da neman naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.

Majiyoyi daga yankin sun ce, da misalin karfe 11 da rabi na daren ranar Asabar ne ‘yan bindigar su ka kira iyalan mutanen, tare da mika bukatar a biya su kudin fansa naira miliyan 25.

Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya auku ne yayin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce ‘yan bindigar sun yi ta harba albarusai a sama, sannan daga bisani su ka yi awon gaba da mutanen hudu da ake zaton duk dalibai ne, sai dai mai magana da yawun jami’ar ya musanta cewa mutanen da aka sace daliban jami’ar ne.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Nassarawa ASP Nansel Ramhan, ya ce babu wanda ya tuntube su daga jami’ar da korafi a kan aukuwar lamarin a hukumance, amma ya ce bayan samun labarin a kafaffen sadarwa, ‘yan sanda sun dukufa wajen kubutar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.