Home Labaru Jami’An Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 10 A Jihar Kaduna

Jami’An Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 10 A Jihar Kaduna

14
0

Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 10 kusa da garin Fatika da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, yayin da wasu maharan su ka jikkata a musayar wuta da jami’an tsaron.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da aka yi garkuwa da shi.

Samuel Aruwan ya kara da cewa, ‘yan bindigar da su ka tsere sun bar mashunan su da wata babbar bindiga da wayoyi da fitilu da kuma layu.

Kwamishin ya cigaba da cewa, an kuma kona wasu daga cikin wuraren da maharani ke ajiye wadanda su ka yi garkuwa da su.