Home Labaru Jam’Iyyar PDP Ta Gudanar Da Tarurrukan Zaben Shugabannin Ta

Jam’Iyyar PDP Ta Gudanar Da Tarurrukan Zaben Shugabannin Ta

12
0

Jam’iyyar PDP ta gudanar da tarurrukan zaben shugabannin ta a jihohin da su ka hada da Adamawa da Oyo da Kwara a karshen mako, sai dai zaben ya bar baya da kura sakamakon yadda rikici ya barke a tsakanin ‘ya’yan ta.

Duk da ya ke an gudanar da taron cikin lumana a jihohin Adamawa da Kwara, amma ba a wanye lafiya a jihar Oyo ba, inda ‘yan jagaliya su ka  kaddamar da hari a kan wani jigon jam’iyyar mai suna Omolaja Alao.

Omolaja Alao dai shi ne shugaban Karamar Hukumar Arewa Maso Gabashin Ibadan, yayin da ‘yan dabar su ka kai masa hari a daidai kofar shiga filin taron.

Rahotanni sun tabbatar cewa, an soke gudanar da irin wannan taron sakamakon tashin hankalin da ya barke a dandalin Tafawa Balewa da ke tsibirin Lagos.

Ana gab da fara zaben ne dai, wani gungun ‘yan dabar siyasa ya  yi dirar mikiya a kan jama’a, lamarin da ya sa tilas aka jingine zaben.