Home Labaru Tsaro Mahara Sun Kashe Sojojin Najeriya Biyar A Zamfara

Mahara Sun Kashe Sojojin Najeriya Biyar A Zamfara

25
0

Rahotanni daga Zamfara na cewa ƴan bindiga sun kashe sojojin Najeriya biyar a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe.

Wanzamai na kan iyakar jihar Zamfara da Katsina a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da maharan suka addaba.

Wasu mazauna yankin sun BBC cewa sojojin sun yi kokarin kai dauki ne a garin na Wanzamai bayan jin karar harbe-harbe.

A cewar wani matafiyi da ya shaidi lamarin ya ce da misalin karfe biyu zuwa uku na dawo daga Abuja bayan na wuce Yankara da ke kan iyakar Katsina da Zamfara, muka tarar jami’an tsaro sun rufe hanya. Daga baya sai muka fahimci cewa mahara ne suka bude wa wata motar sojoji wuta kuma suka kashe duka sojoji biyar da ke ciki.”

” Kuma ganin cewa babu sadarwa yankin muna sa ran sojojin na sintiri ne maharan suka far musu suka bude musu wuta suka kuma kwashe musu makamai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa su suka taimaka wa yan sandan da suka kwashe gawawwakin sojojin.

Sama da wata daya Kenan da katse sadarwa a wasu yankunan jihohin Zamfara da Katsina, tare da rufe kasuwannin mako-mako a wani bangare na tsaurara matakan yaki da yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.