Home Labaru Gobara Ta Tashi A Dandalin Bikin Fina-Finai A Masar

Gobara Ta Tashi A Dandalin Bikin Fina-Finai A Masar

13
0

Gobara ta tashi a dandalin taron bude baje kolin fina-fanai na kasar Masar, lamarin ya sa aka nemi soke bikin.

Wutar ta tashi ne kasa da awa 24 kafin fara taron bude bikin, da aka shirya baje kolin fina-finan 80 na kasashen Larabawa da kasashen duniya.

Daya daga cikin wadanda suka shirya bikin, Ola El-Shafei ya ce, Har yanzu suna cikin zullumi, amma suna yiwa Allah godiya bayan da suka tsira da ransu,

Tashin wutar ta haifar da shakku game da fara bikin, amma an samu an kashe “Wutar da ta lalata wani bangare na babbar rumfar da aka shirya,” wata taron na El Gouna.

An garzaya zuwa asibiti mutum 15 da suka galabaita a sakamakon shakar numfashin da ta turnike bayan tashin gobarar, inji wani jami’in tsaro.

Taron fim din wanda attajirin Afirka, Samih Sawiris, ya karbi bakuncin taurarin masana’antar fim din Hollywood na kasar Amurka, ciki har da Forest Whitaker da Owen Wilson a shekarun baya.