Home Labaru Sunday Igboho Na Fama Da Ciwon Koda A Gidan Yari  

Sunday Igboho Na Fama Da Ciwon Koda A Gidan Yari  

11
0
Sunday

Lauyan mai fafutukar kafa kasar Yarbawannan a Najeriya Sunday Igboho,  ya ce gwaji ya nuna cewa akwai alamun yana dauke da ciwon koda ko na huhu.

A hira da sashen Yarbanci na BBC Barista Yomi Aliyyu ya ce wanda yake karewar ya kamu da cutar ne yayin da ya ke tsare a Jamhuriyar Benin.

A cewarsa har ma an garzaya da shi asibiti bayan da rashin lafiyarsa ta yi tsanani.

Jami’an tsaro a Najeriya sun kai samame a gidan Sunday Igboho da ke garin Ibadan na jihar Oyo da ke Kudanci a ranar 1 ga watan Yulin 2021, inda suka kama mutun 12.

Sai dai a ranar 16 ga watan Yuli ne aka kama Mr Igboho a Coutonou da ke Jamhuriyar Benin ind ayanzu haka ake tsare dashi.

Rahotanni sun nuna cewa yana kokarin tsallakawa Jamus ne a lokacin.